ABNA24 : Hezbollah ta dai shigar da karar wani tsohon dan majalisar dokokin kasar da kuma wata jam’iyyar siyasar kasar kan yi mata wannan zargin.
A ranar 4 ga watan Agusta da ya gabata ne wata fashewa ta auku a tashar ruwa ta birnin Beirut, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 200 da kuma jikatar wasu 6,500 da kuma haifar da babbar barna a birnin.
Bayan fashewar data auku jama’ar kasar da dama sun zargi mahukunta da manyan ‘yan siyasar kasar.
342/